Shugaban Hukumar kula da ayyukan yansanda ta kasa Alhaji Musiliu Smith ya tabbatar da ajiye shugabancin hukumar da safiyar yau.
Mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani,shi ne ya tabbatar da ajiye aikin shugaban ga manema labarai da a Abuja ,inda yace shugaban ya ajiye aikin nasa a sakamakon dalilai na rashin lafiya.
Ani ya kara da cewa hukumar za ta fitar da sanarwa a hukumance dangane da Al'amarin.
Idan ba a manta ba,Wata majiya daga hukumar ta bayyana wa manema labarai cewa an rubutwa shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar ajiye aikin nasa kuma tuni aka amince da hakan.
Nan kuma Wata kungiyar farar hula mai rajin tabbatar da bin doka da bada shawarwari mai suna RULAAC a takaice, Ta yaba da murabus din da Musliu Smith yayi daga kan matsayin Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Sanda ta kasa.
Rahotanni sun baiyana cewa Smith ya yi murabus ne a ranar Laraba sakamakon shawarar da kwamitin hukumar ya bayar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, Ta yi maraba da matakin da Musliu Smith ya dauka, inda aka maye gurbinsa da mai shari’a Clara Ogunbiyi mai ritaya, wadda ta kasa kwamishiniyar shari’a a hukumar.
Shugaban kungiuyar Okechukwu Nwaguma yace sun sha nanata cewar nada tsohon sufeton yansanda na kasa a matsayin shugaban hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kasa, ya karya ka’idar doka da kuma makusudin da yasa aka kafa hukumar.