On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Shugaban Gwamnatin Jamus Zai Ziyarci Najeriya

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai ziyarci Najeriya a watan Oktoba a wani mataki na kara karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale, a wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, ya ce an cimma matsayar ne a gefen taron G-20 a birnin New Delhi na kasar India, inda shugaba Bola Tinubu da jagoran na Jamus suka gana.

Sanarwar ta ambato Scholz na yabawa da  damar na ciyar da huldar tattalin arzikinsu gaba, yana mai cewa kasuwar Najeriya ta kasance wadda babu kamarta kuma kamfanonin Jamus na da tarihi a Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, bayan ganawa da jagoran na Jamus, Tinubu ya kuma tattauna da takwaransa na Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol wanda ya yabawa shugaban kan jagorancin yankin yammacin Afirka .