shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin za su tattauna kan yakin Ukraine da sauran batutuwan kasa da kasa a taronsu na ranar Alhamis.
Kasashen biyu za su gana ne a kasar Uzbekistan a wani taron koli da zai mada hankali kan dangantarsu da kasashen yammacin duniya. Mista Xi yana yin ziyararsa ta farko zuwa ketare tun bayan barkewar cutar korona.
A yau Laraba ne Xi ya fara ziyarar kwanaki uku a kasar Kazakhstan.
Daga nan zai gana da Mista Putin a ranar Alhamis a taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a Samarkand, wanda zai gudana daga 15 zuwa 16 ga watan Satumbar da muke ciki.