Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a yau Litinin, 31 ga Yuli, 2023 da karfe 7 na yamma.
An tabbatar da jawabin ta cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban shawara kan ayyuka na musamman da sadarwa Dele Alake ya fitar.
Sanarwar ta umarci gidajen Talabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai na zamani da su jona jawabin daga gidan talabijin na kasa NTA da gidan Rediyon tarayya.