Da alama rudanin siyasa da aka shafe makonni a jihar Rivers ka iya karewa, sakamakon cimma matsaya a ranar Litinin bayan wata ganawa da dukkanin bangarori suka yi da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar Villa da ke Abuja.
Taron ya kuma samu halartar gwamna Siminalayi Fubara, da magabacinsa, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Rivers da Peter Odili sai Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettim, da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila da wasu sarakunan gargajiya daga jihar.
Sai dai sulhun da aka cimma a taron ya samu sahannun Fubarada Wike da Amae-hule a daidai lokacin da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya sanya hannu akan takardar inda bangarorin dake rikici da juna suka amince a janye duk wasu kararraki da aka shigar kotuna cikin gaggawa.
Jam’iyyun da ke cikin rikicin sun kuma yanke shawarar amincewa da shugabancin Martin Amae-hule da ‘yan majalissa 26 wadanda kwanan nan suka fice daga PDP zuwa APC a majalisar dokokin jihar Rivers tre da watsi da shugabancin Edison Ehie.
Sauran bangarori da aka cimma masalaha taron da aka yi a Abuja sun hada da biyan alawus-alawus da alawus-alawus na daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers kuma dole ne a mayar da ma’aikatansu cikin gaggawa sannan kuma daga yanzu Fubara ba zai tsoma baki cikin kudaden da majalisar jihar za ta samu ba.
Majalisar Dokokin Jihar Rivers za ta zabi inda za su zauna su gudanar da harkokinsu na majalisar ba tare da tsangwama ko hantara daga bangaren zartarwa na gwamnati ba.
Gwamna Fubara zai sake gabatar da kasafin kudin jihar ga majalisar dokokin jihar Rivers da aka tsara yadda ya kamata sannan kuma za a sake mika sunayen kwamishinonin da suka yi murabus ga majalisar domin amincewa.
A karshe an kuma yanke shawarar cewa bai kamata a samar da kwamitin riko na kananan hukumomi a jihar Rivers ba, don haka an soke matakin rusa shugabannin kananan hukumomi.