Shugaban kasa Bola Tinubu, ya gana da gwamnonin jihohin Najeriya biyar da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar a fadar gwamnati da ke Abuja, domin duba hanyoyin da za a bi wajen maido da mulkin dimokradiyya a Nijar.
Majiyoyin fadar shugaban kasar sun ce taron na daga cikin matakan tuntuba da gwamnatin Tinubu ke yi kan tunkarar hanyoyin siyasa a Nijar.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Ahmed Aliyu na Sokoto da Umar Namadi na Jigawa da Mai Mala Buni na Yobe da Idris Nasir na Kebbi da Dr Dikko Radda na jihar Katsina.
Ba a bayyana sakamakon ganawar da aka yi ba wadda ta kasance ta Sirri har zuwa lokacin hada wannan rahoto a safiyar yau.