Ministan ayyuka, Injiniya Dave Umahi, ya ce ya samu amincewar shugaban kasa Bola Tinubu kan matakin da ma’aikatar sa ta dauka na yin amfani da Kankare wajen inganta Tituna a kasarnan.
Umahi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a fadar gwamnati da ke Abuja, bayan ya gana da shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar yin amfani da wannan sabuwar hanya ta Kankare maimakon amfani da kwalta da aka dade ana amfani da ita.
Ministan ya kuma yi zargin cewa ya gano akwai masu hada kai a cikin ma’aikatar da ke aiki da ‘yan kwangila da suka kalubalance shi da gwamnatin tarayya kan zabin amfani da Kankare wajen yin Tituna.