On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Shugaba Tinuba Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Makamashi Ta Najeriya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Dr Abdullahi Mustapha a matsayin Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, ta ce shugaban kasar na saran Mustapha zai bada gudunmawa sosai a yunkurin gwamnatinsa na karkata hanyoyin samar da makamashi a kasar nan.

Mustapha ya yi aiki sama da shekaru goma a Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya tare da gogewa sosai a fannin makamashi da fasaha.