On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shugaba Tchiani Na Jamhuriyar Nijar Ya Kaddamar Da Babban Taron Muhawara Na Kungiyar Hadin Kan 'Yan Jarida Na Afirka Masu Amfani Da Harshen Hausa.

Shugaban 'kasar Nijar kuma shuban majalissar ceton 'Kasar, Birgediya Janar Abdorahamane Tchiani ya kaddamar da babban taron kwana 3 na kungiyar hadin kan 'yan Jarida na kasashen Afirka masu amfani da harshen Hausa bisa Jagorancin Hajiya Maryam Lawalli Sarkin Abzin.

Babban taron muhawara karo na farko akan zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar harshen hausa da tabbatar da 'Yancin kasashen Afirka a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar na samun halartar kasashe 11.

Tchiani wanda ya samu wakilcin Fira-ministan Nijar Ali Muhamane Lamine Zeine, ya bukaci gudunmawar 'yan Jarida a nahiyar wajen samun cigaba a yankin.

Shugabar Kungiyar ta hadin kan 'yan Jarida na kasashen Afirka masu amfani da harshen Hausa, Hajiya Maryam Lawalli Sarkin Abzin, ta koka akan yadda Labaran karya musamman a shafukan sada zumunta ke kawo cikas ta bangarori da dama a Afirka.

Ta bukaci a dawo da martabar nahiyar ta hanyar kungiyar sannan ayi taka tsan-tsan da masu zagon 'kasa.

Cikin mahalarta taron daga Najeriya akwai Major Janar Hamza Al-mustapha mai ritaya da Hajiya Naja'atu Muhammad da sarakunan Awe da Machina da sarkin Talatar Mafara da dai sauran su.