Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un na Koriya na shirin yin balaguro zuwa kasar Rasha a cikin wannan watan domin ganawa da shugaba Vladimir Putin, kamar yadda wani jami'in Amurka ya shaidawa manema labarai.
Jami'in ya ce shugabannin biyu za su tattauna kan yiwuwar baiwa kasar Rasha makamai domin taimakawa yakin da take yi a Ukraine.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ainihin wurin da aka shirya ganawar ba, kuma babu wani karin haske kan wannan rahoto da aka fitar.
Wasu Majiyoyi sun shaida wa jaridar New York Times cewa, mai yiwuwa shugaba Kim Jong Un zai yi tafiyar ne a cikin jirgin kasa mai sulke.
Yiwuwar ganawar ta zo ne bayan da fadar mulkin Amurika ta White House tata ce ta samu sabbin bayanai da ke nuna cewa akwai tattaunawar samar da makamai tsakanin kasashen biyu.