Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin hako man fetur a kogin Kolmani na II dake yankin Arewa maso gabas ranar talat mai zuwa.
Jami’an Kamfanin Man Fetur na NNPC Limited sunce za a fara aikin hakar mai ka’in da na’in a kogin na Kolmani da ke cikin yankunan Bauchi da Gombe bayan kaddamarwa.
A watan Oktoba na shekarar 2019, kamfanin NNPC ya sanar da gano ma’adanar iskar gas a rijiyar Kolmani ta II. An dai gano tarin arzikin man fetur a jihohin biyu shekaru biyu da suka gabata.
Kararamin ministan man fetur na ƙasa Timipre Sylva, yace a gudanar da bikin fara tono man ranar Talata 22 ga watan da muke ciki na Nuwamba Inda shugaba Buhari tare da wasu daga cikin ministocinsa za su halarta.
A shekarar 2016 ne kamfanin mai na ƙasar NNPC ya ƙaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin ƙasarnan, abin da ya kai ga gano ɗimbim albarkatun man fetur ɗin a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Neja..