Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na ganin an samu sauyi cikin sauri da dabaru domin komawa amfani da makamashi dake samar da lantarki.
Ya ce hakan zai kasance ne a matsayin tallafawa kokarin da ake yi a duniya na kiyaye muhalli.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yace Buhari ya sanar da hakan a wata ganawa da shugabanni da suka yi kan sauyin yanayi wanda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya kira.
A wajen taron, shugaban na Najeriya ya jaddada cewa, a watan Agustan wannan shekara gwamnatinsa ta kaddamar da wani shiri na samar da wutar lantarki a gida, yana mai cewa tsari ne na cimma nasarar kawar da fitar da hayaki mai zafi zuwa shekarar 2060.
A cewarsa, an yi hakan ne da nufin tabbatar da samun raguwar gurbatar yanayi tare da daidaita manyan burin nci gaba bisa gaskiya da adalci.