On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Shugaba Buhari Na Najeriya Ya Sha Yabo Daga Shugabannin Nahiyar Afirka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin makon jiya, ya samu karbuwa a zukatan ’yan uwansa shugabannin kasashen Afirka a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, wadanda suka bada sheda masu mai kyau game da halayensa na jagoranci.

Shugabannin kasashen Afirka sun je birnin Yamai ne domin halartar taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka kan bunkasa masana'antu da habaka tattalin arziki.

Shugabannin Afirka sun yi amfani da damar taron wajen halartar bikin kaddamar da littafin ‘Muhammadu Buhari: kan Kalubalen Shugabanci a Najeriya.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin, shugaba Mohamed Bazoum na jamhuriyar Nijar ya bayyana shugaban na Najeriya a matsayin mai kishin kasa kuma mai kishin demokradiyya.

Shima mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, yace yana jin dadin aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Adesina, tsohon babban editan jaridar Sun, an nada shi a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa a watan Mayu na shekarar  2015 jim kadan  bayan Buhari ya karbi mulki.

An sake nada shi ne a watan Agustan 2019 bayan an zabi Buhari a karo na biyu.

Da yake magana a karshen mako, Adesina ya ce yana godiya ga shugaban kasa saboda ganin  cancantarsa amatsayin wanda zai yiwa  Najeriya hidima a wannan matsayi.