Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan sauyin yanayi daga manyan kasashen da suka ci gaba domin tunkarar matsalar sauyin yanayin a Afirka.
Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi ya yi wannan kiran a ranar Litinin a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP27 na shekarar 2022.
Taron neman kawo sauyi da tsaftace Makamashi ya baiwa Najeriya dama don bayyana yunƙurin magance yanayi da damuwar yanayi.
Saboda haka ya yi kira da a gaggauta daukar matakai daga kasashen da suka ci gaba wadanda ke fitar da mafi yawan hayakin da ke shafar yanayi a Afirka.