Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya bayar da umarnin gaggauta fitar da tan dubu 200 na abinci daga rumbun abinci na gwamnatin domin rabawa al’umma da nufin rage radadin cire tallafin man fetur da ya haifar da tsadar rayuwa.
Haka kuma, shugaban ya bada umarnin fitar da tan dubu 250 na takin zamani domin rabawa manoma tare da ingantattun iri domin tunkarar aikin noma da samar da abinci.
Tinubu ya bayyana wadannan matakai ne a ranar litinin lokacin da ya ke yi wa ‘yan kasa kasa jawabi dangane da halin tsadar rayuwa da ake fuskanta.
Shugaban kasar ya kuma ce gwamnatin sa ta ware naira biliyan 200 domin zuba biliyan hamsin-hamsin wajen bunkasa noman masara da shinkafa da alkama da kuma rogo a fadin Najeriya.