Jam’iyyar APC ta ce shirye-shirye sun kusan kammala domin fara yakin neman zaben Tinubu da Shettima na shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Darakta-Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023 gwamna Simon Lalong, shine ya bayyana haka bayan ya duba kayayykin da aka samar a shalkwatar yakin neman zaben da ke Abuja.
Mai magana da yawun gwamnan Dr Makut Macham, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar jiya a Jos, yace sakataren kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, James Faleke, ya tarbi Lalong a shalkwatar.
Macham ya ce shugaban ya kuma gana da wasu ma’aikatan majalissar yakin neman zaben, a wani bangare na kokarin tabbatar da wata babbar tawaga ta yakin neman zaben.