On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Shirye-Shiryen Bikin Auren Zawarawa Na 2023 Na Cigaba Da Kankama A Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano tace tana cika alkawarin da ta dauka na daukar nauyin Auren Zawarawa da samari dqa ‘yan mata yayin da hukumar Hisbah ta jihar ta sayo kayan daki da  kayan abinci da  kayan sawa domin bikin auren.

Hukumar ta ce ta kashe sama da Naira miliyan 800 wajen sayen kayayyakin a wani bangare na shirye-shiryen daurin auren, mutane sama  da dubu 1.

Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tabbatar da haka a lokacin da yake duba kayayyakin.

Ya ce amare zasu samu kayan daki da katifa da matashin kai, da kuma jarin Naira dubu 20 domin fara kasuwanci.

A cewarsa, irin wannan karamci zai taimaka matuka wajen dakile munanan dabi’u a cikin al’umma.