Dan wasa Kevin De Bruyne ya farkewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kwallon da Real Madrid ta fara zura mata a raga a ranar Talata, a wasan da suka tashi 1 da 1
A wasansu na zagayen farko na gasar cin kofin zakarun Turai na UEFA, dan wasan tsakiyar Manchester City ya farke kwallon ne a minti na 67.
Hakan ya faru ne bayan Vinicius Junior ya fara zura kwallo a ragar mancheste city a zagayen farko na wasan.
Manchester City ce ta mamaye wasan a farkon amma Real Madrid ta karbe ragamar wasan daga baya.
Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan zagaye na biyu a ranar Laraba mai zuwa.