Manyan kasuwannin Kano sunyi cikar kwari a jiya yayin da al’ummar Musulmi da dama ke sayen kayyakin bukatu daban-daban gabanin Idin Babbar Sallah da za’a yi a yau
Tun a ranar Asabar ne mazauna sassan Kano ke tururuwa zuwa kasuwannin dabbobi domin Sayen raguna da zasuyi layya, yayin da wasu kuma suka shagaltu da siyan sabbin tufafi da takalma da sauran kayayyaki ga iyalansu.
Saboda yawaitar masu Sayayya yawancin wuraren kasuwanci na wucin gadi suma suka makil, ana sayar da kayan kwalliya, da sauran kayan ado na mata da yara.
Wakilinmu Victor Christopher da ya ziyarci Kasuwar Yankaba da wasu rumfunan wucin gadi ya lura da cewa farashin tumatur ya yi tashin gwauron zabi.
A jiya an sayar da kwano daya na tumatur akan Naira dubu 2 yayin da kwandon kuma akesayarwa akan Naira dubu 35.
Sai dai farashin raguna da shanu ya tashi daga Naira dubu 100 zuwa dubu 250 da dubu 400 zuwa dubu 800.