On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Shigar Mata Cikin Sana'ar Gyaran Waya Zai Warware Matsalolin Zamantakewa Da Tattalin Arziki - Abdallah Uba Adamu

Wasu kungiyoyin cigaban al’umma sun kafa tubalin shigar da Mata da ‘Yan mata cikin sana’ar gyaran waya a Kano domin magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki.

Wannan tunani ya biyo bayan bikin ranar mata ta duniya na 2023 wanda babban malami a tsangayar sadarwa da nazarin harkokin yada labarai, Abdullah Uba Adamu, ya yi rubutu a shafin sada zumunta kan yadda a irin wannan biki ake maida hankali akan matan da suka shahara a idon duniya maimakon matan da suke cikin lungu da sako kuma suke aiki tukuru wajen dawainiya da yara musamman wadanda mazajensu suka mutu ko wadanda mazajen suka gudu.

Adamu, yace rubutunsa akan labarin wani yaro da mahaifiyarsa mai sayar da Fura wadda ta tsayawa yaron domin cimma burinsa na zamamai tukin jirgin sama ya ja hankulan mutane ciki harda tsohon ministan kudi Dr Shamsudeen Usman da Injiniya Yunusa Zakari (YZ) shugaban cibiyar CITAD.

Ya ce bayan tatttaunawa da nazari yaga gyaran waya sana’ace da ake bukata a kullum kasancewar wayar ta zama ruwan dare kuma akasari mata ba sa samun damar fita domin kai gyaran waya saboda wasu dalilai ko dai na al’-ada ko kunya baya ga hatsarin da suke fuskanta naga bata garin matasa ko fargabar fitar siirin dake cikin wayoyin na su.

Daga karshe an zabi kai horon unguwar Sani Mainagge saboda dacewarsu da wayewa da kumakarsashinsu akan harkokin fasahar zamani.

Da yake jawabi yayin kaddamar da horon ga Mata da ‘yan Mata da aka zabo,  Abdallah Uba Adamu ya yi kira ga dalibai mata matasa da su rungumi salon zamani da ya zama ruwan dare domin su zama masu dogaro da kai a nan gaba, yana mai  cewa rungumar shirin zai taimaka musu ko da sun zama matan Aure.

Ya ce, a matsayinsu na mata, matasa  za su iya zama hanyar samar da ayyukan yi  ta hanyar horan da suka samu, ya kara da cewa babu wata fasaha da kirkire-kirkire da za’aiya cewa sunyi kankanta wajen inganta rayuwar bil’adama.

Da yake jawabi tun da farko, babban daraktan cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma CITAD, Malam Yunusa Zakari Ya’u wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Mallam Ahmad Yakasai, ya ce an bijiro da wannan horon ne domin karfafawa mata  gwiwa kan muhimmancin  dogaro da kai kammar yadda cibiyar ta dukufa wajen samar da cigaban al’umma ta hanyar fasahar sadarwa.