‘Yar wasa Serena Williams ta sanar da cewa ta na shirin yin murabus daga fagen wasan kwallon tennis, inda ta ce za ta janye daga wasan bayan gasar US Open.
‘Yar kasar Amurkar da ta lashe manyan kofunan Grand Slam har guda 23 ta ce za ta shiga wasu harkokin na daban da ke da mahimmanci a gare ta, ta na mai cewa ba ta kaunar kalmar ‘murabus’.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, Williams ta ce ‘’ta fara kirge na lokacin da za ta yi adabo’’.
Williams ta dawo wasan tennis ne a gasar Wimbledon a watan Yuni bayan lokaci mai tsawo da ta kwashe ta na jinyar raunin da ta samu, inda har ana ta yada jita jitar cewa za ta yi murabus.
(Karin Magana:….Da muguwar rawa gwamma kin tashi)
Wlliams ta ce za ta fafata a gasar US Open a watan Agusta.
Margaret Court ce kawai ke gaban Williams wajen lashe manyan kofunan wasan tennis, inda ta ci 24.