Kungiyar nan mai rajin kare hakkin dan adam da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da ma’aikatun gwamnati SERAP ta kai karar Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda kin yin biyayya ga umarnin da kotu ta bayar, inda ya ya haramta yin amfani da tsohuwar naira 500 da kuma dubu 1.
Lauyoyin kungiyar Ebun-OluAdegboruwa da Kolawole Oluwadare ne suka shigar da karar a madadin kungiyar ta SERAP a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja.
SERAP na neman kotu ta tantance ko umarnin da shugaba Buhari ya bayar na haramta yin amfani da tsohuwar naira 500 da da dubu 1 bai dace da tsarin kundin tsarin mulkin kasa da kuma umarnin da kotun koli ta bayar,
SERAP na kuma neman kotun ta bada wani umarni na wucin gadi da zai hana shugaba Buhari da Babban bankin kasa CBN ci gaba da aiwatar da umarnin hana yin amfani da tsofaffin takardun kudi.