Kungiyar nan mai rajin kare hakkin dan adam da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da Ma’aikatun gwamnatin tarayya, SERAP ta kai karar majalisar dokoki kasa gaban kotu, saboda shirinta na raba sabbin motoci kirar Prado SUV ta naira milyan 130 ga kowanne dan majalisar dokokin tarayya tare da jagororin majalisar.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a daren jiya, ta shigar da karar batare da bata wani lokaci ba, domin ganin kotun ta hana raba motocin alfarmar ga ‘yan majalisar dokokin tarayya, wanda jimillar kudinsu zai kama naira milyan dubu 40.
Kungiyar ta SERAP ta shigar da karar ne bayan da ‘yan majalisar dokokin suka matsa lamba kan cewar dole ne sai an saya masu motocin, duk kuwa da shan sukar da suke fuskanta daga yan Najeriya.
Sai dai a lokacin da yake kare batun raba sabbin motocin ga ‘yan majalisar, Kakakin majalisar wakilai, Rotimi Akin, Y ace al’adar zauren majalisar ce sayan motoci tare da raba su ga ‘yan majalisar domin gudanar da aikin majalisa.