On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

SERAP Ta Bukaci Tinubu Ya Hana Ministocinsa Cigaba Da Karbar Pansho Na Tsaffin Gwamnoni

Kungiyar SERAP ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci tsaffin gwamnonin da ke rike da mukamin minista a gwamnatinsa da su daina karbar kudaden fansho da manyan motoci da sauran alawus-alawus daga jihohinsu.

SERAP ta bukace shi da ya umarci tsoffin gwamnonin da su gaggauta mayar da duk wani kudaden fansho da alawus-alawus da suka karba tun bayan barin aiki zuwa asusun gwamnati.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare a karshen mako.

Tsoffin gwamnonin da a yanzu suka  zama ministoci a gwamnatin Tinubu sun hada da Badaru Abubakar da Nyesom Wike da  Bello Matawalle da  Adegboyega Oyetola da David Umahi.

Sauran sun hadar da Simon Lalong da Atiku Bagudu; da Ibrahim Geidam.

……