Kungiyar tabbatar da adalci da yaki da rashawa SERAP ta yi karar shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.
Matakin na baya-bayan nan da SERAP ya biyo bayan zargin shirin da ‘yan majalisar suka yi ba bisa ka’ida ba na kashe Naira billiyan 40 domin sayen wasu manyan motoci 465 masu sulke ga mambobin majalissar da manyan jami’an gwamnati, da kuma Naira billiyan 70 a matsayin maraba ga sabbin mambobin.
SERAP na neman a bada umarnin hana Akpabio da Abbas kashe Naira biliyan 40 wajen siyan motoci 465 har sai an yi nazari kan tasirin tattalin arzikin akan talakawan Najeriya miliyan 137.
Wannan kara na zuwa ne a daidai lokacin da Akpabio ya bayyana cewa magatakardan majalisar ya aika da alawus - alawus a cikin asusun bankuna daban-daban na Sanatoci.