Kungiyar dake rajin tabbatar da adalci da yaki da rashawa a Najeriya SERAP ta bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da kada ya amince da wani shiri da ake zargin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike na tsarawa na gina gidan Alfarma ga Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Disamba mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, kungiyar na bukatar Akpabio ya yi watsi da shirin da Wike ke yi na kashe Naira biliyan 15 domin gina ‘gidan Kasaita ga Shettima.
Sanarwar ta yi kira ga Akpabio da ya tabbatar da ayyukan sa ido kan tsarin mulki na Majalisar Dattawa ya kuma yi watsi da bukatar kashe Naira billiyan 2.8 kan tallata Hukumar cigaban birnin Abuja da sauran tanadin kashe kudi na almubazzaranci a cikin kwarya-kwaryan kasafin 2023 da kuma kasafin 2024 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.