Hukumomin kasar saudiyya sun aiyana ranar Asabar mai zuwa 13 ga watan Augustan da muke ciki, a matsayin rana ta karshe da Alhazan da suka yi aikin hajjin bana zasu kammala ficewa daga kasar.
Ma’aikatar kula da aikin Hajji da Umrah ta kasa mai tsarki, Tace Kanfanonin kula da jigilar mahajjata ya zama wajibi su kammala kwashe mutanensu kafin karewar wa’adin.
Kazalika ta baiyana cewa ya zama tilas kanfanonin suyi aiki da ka’idojin tafiye-tafiye da aka tsara a aikin hajjin bana.
Milyoyin Mahajatta ne dai suka sauke farali a aikin hajjin bana, wanda aka dakatar tun bayan bullar cutar Korona shekaru biyu da suka gabata.