Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya taya Zabbben Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Murna bisa nasarar da ya samu ta lashe zaben Gwamnan Kano a zaben da aka gudanar ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023
Cikin wata sanarwa daga Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa ta bayyana cewa al'ummar kasar nan sun karbi tsarin mulkin damokaradiyya da matuqar muhimmacin idan akayi la'akari da yadda suka futo domin jefa kuri'unsu kamar yadda tsarin mulki ya bada dama.
Sanawar ta kuma godewa malamai da Limamai da sauran Al'umma bisa addu'ar zaman lafiya da suka dunga yi kafin da kuma bayan gudanar da zaben.
Daga nan fadar Masarautar ta Kano tayi nasiha tare da kira ga sabon gwamnan daya hada kai da dukkanin rukunin al'umma wajen tafiyar da gwamnati, domin yin hakan zai taimaka wajen kyautata rayuwar al'umma da kuma kawo cigaban da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano har ma da sauran sassan Najeriya.
Shima mai martaba Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Gaya da yake taya Abba murnar lashe zaben, ya ce yana da kwarin guiwar zai samar da shugabanci mai nagarta.
Wasikar ta ce, “A madadina da iyalina da daukacin al’ummar Masarautar Gaya, muna farin ciki tare da taya ku murnar nasarar da kuka samu a zaben gwamnan Jihar Kano da aka yi.
Sarkin Rano ma Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ya aike da na sa saƙon tare da fatan Allah ya taya sabon shugaban riƙo da shugabancin mutanen Kano.
Har ila yau, mai martaba sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar III bisa wakilcin dan majalissar masarautar kuma hakimin Madobi Alhaji Sale Musa Sale Kwankwaso ya aike da wasikar taya murna ga tsohon gwamnan Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso kan Nasarar jam’iyyar NNPP a zaben gwamnan Kano.