On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Sarki Sunusi Murabus Ya Gana Da Shugaban Kasa Tinubu

A jiya ne sarkin Kano Murabus Muhammadu Sanusi na biyu, ya kai wa shugaba Bola Tinubu ziyara a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa dake Abuja.

Sarki  Sanusi ya isa Villa ne sa’o’i kadan  bayan  da  shugaban kasar ya kaddamar da majalisar  bunkasa  tattalin arzikin kasa.

Muhammadu Sanusi na biyuwa wanda ya kasance  masanin tattalin arziki,  ya dauki tsawon lokaci  yana  fafutukar  ganin an cire tallafin man fetur.

Wannan ita  ce ganawa  ta  farko  tsakanin  Tinubu da Sanusi a  fadar  shugaban kasa  ta  Aso Rock.

Idan  ba’a manta  ba,  mutanen biyu sun  gana  a Faransa a makonnin da suka   gabata.