A daren jiya ne Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi na biyu ya ziyarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadarsa dake Villa Abuja bayan ganawar da yayi da jagororin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.
Rahotanni sun baiyana cewa Sarki Sanusi ya je jamhuriyar Nijar ne bisa radin kansa ba wakilcin gwamnati ba, inda ya gana da jagoran mulkin sojan kasar domin bude kofar tattaunawa.
Sarki Sanusi ya isa fadar Villa ne da misalin karfe 8 da minita 25 na dare bayan wata babbar tawagar Malamai kasa ta gana da shugaban kasar.
Kafin dawowarsa Najeriya sarkin kano Murabus Muhammadu Sanusi na biyu ya yiwa manema labarai karin haske kan makasudin zuwansa jamhuriyar Nijar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da manyan jami'an diflomasiyya na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma na kungiyar ECOWAS za su gana yau a Abuja yau domin daukar matakan da suka da ce akan juyin mulkin da aka yi a kasar ta Nijar.