On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Sardaunan Dutse Dr Bello Maitama Yusuf Ya Rasu

Allah ya yi wa tsohon minista kuma tsohon sanata, Alhaji Bello Maitama Yusuf, Sardaunan Dutse rasuwa yana da shekara 76.

Sardaunan dutse wanda dan kasuwa ne kuma dan Siyasa, haifaffen Gwaram ne dake  Jihar Jigawaya rasu a Kano  ranar juma'a 13 ga watan Octoba 2023 bayan fama da rashin lafiya.

Maitama Yusuf, ya rike mukamin ministan harkokin cikin gida a shekarar 1978, sannan ya zama ministan kasuwanci a shekarar 1982.

Ya taba zama Sanata mai wakiltar Jigawa ta Kudu maso Yamma a tsakanin 1999 zuwa 2007, a jam'iyyar ANPP daga baya ya koma jam’iyyar PDP.

Ya kuma tsaya takarar gwamnan jihar Jigawa a shekarar 2007.

Guda daga cikin zuri’ar marigayin Alhaji Abdullahi Bello ya tabbatarwa Arewa Radio cewa za’ayi Jana’izar Bello mai taima a fadar mai martaba sarkin Kano bayan Sallar Juma’a a yau.

Bello maitama ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya ya 10 maza 5 da mata 5.