On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sanusi Da Falae Sun Bukaci Shugaba Tinubu Ya Sauka Daga Mukaminsa Ministan Man Fetur Na Najeriya

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mallam Muhammadu Sanusi na II, ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya rike ofishin ministan albarkatun man fetur.

Da yake jawabi a wajen taron shugabannin bankunan da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja, Sanusi ya ce irin wannan tsari zai sa kasar nan ta shiga wahala wajen rike kamfanin man fetur na Najeriya.

Sanusi wanda shi ne gwamnan babban bankin kasa  daga watan Yunin 2009 zuwa Fabrairu 2014, ya caccaki kamfanin NNPC Limited da gazawa wajen  tura isassun kudaden waje a cikin asusun gwamnati duk da cire tallafin man fetur.

Ya jaddada bukatar daidaita kasuwar musayar kudaden waje, inda ya ce manufofin hada-hadar kudi a cikin shekaru takwas da suka gabata sun haifar da hauhawar farashin kayayyaki da koma bayan tattalin arziki a kasarnan.

Shima, wani dattijon kasa  kuma tsohon ministan kudi, Cif Olu Falae, ya ce ba sai shugaban Najeriya ya zama ministan man fetur ba, yana goyon bayan matsayar tsohon gwamnan CBN, Muhammadu Sanusi.

Falae ya kuma yi amanna cewa, nada ministan man fetur zai sa a samu wanda za a tuhuma  a lokacin da al’amura suka tabarbare.

Idan za'a iya tunawa  tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rike mukamin ministan mai a lokacin da yake kan Mulki  inda shima a

 Bola Tinubu yabi Irin tsarin.

Amma dattijon ya ce ya kamata ma’aikatar man fetur ta samu minista ba shugaban kasa ba.