Sanatocin jam’iyyar APC 22 da suka harzuka dangane da yadda sakamakon zaben fidda gwaninsu ya kasance, harma suke shirin ficewa daga cikin jam’iyyar, sun jingine aniyar tasu.
Hakan na zuwa ne a yayin da sanatacin suka gana da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yau a Abuja.
Jagoran Sanatocin, Sanata Orji Kalu wanda ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar, Ya baiyana cewa Sanatocin sunji rashin dadin yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin.
Da yake gabatar da jawabi a yayin ganawar da suka yi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sanatocin dasu janye shirinsu na ficewa daga cikin jam’iyyar.
Shugaban yace sauyin sheka babbar barazana ce ga rinjayen da jam’iyyar APC ke dashi a majalisar Dokoki ta kasa.