Wasu Rahotanni na baiyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekaru na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP mai kayan Marmari zuwa Jam’iyyar PDP mai Alamar Lema, biyo bayan wata ganawa da suka yi da Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
A lokacin da wasu jagororin jam’iyyar NNPP, wadanda suka da hada Abba Kabir Yusuf Dan takararta na gwamna da Dan Takarar Sanatan Kano ta kudu Kawu Sumaila da kuma Dan takarar majalisar Wakilai Kabiru Rurum suka samu labarin yunkurin sauyin shekar sanata Shekarau, sunyi gaggawar neman ganawa dashi a daren juma’a, amma kuma sanatan bai yarda sun ganshi ba.
Jaridar Daily Nigeria ta cigaba da cewa, wasu majiyoyi masu tushe sun baiyana cewa shekarau yayi ganawa daban daban tare da Atiku Abubakar da kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa Ifenyi Okowa da shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchia Ayu, inda suka kammala dabdale komi a tsakaninsu, wanda ake saran nan bada jimawa ba tsohon gwamnan zai aiyana ficewarsa daga NNP.
Majiyar tace yunkurin ficewar baya rasa nasaba da yadda sanata kwankwaso ya gaza cika masa alkawarun da suka kulla tsakaninsu tun kafin ya koma jam’iyyar NNPP daga jam’iyar APC, bayan takun sakar data gitta tsakaninsa da Gwamna Ganduje.
Sai dai kuma jaridar Solacebace tace wata majiya daga gidan shekarau tace kwamitin shura yayi taro na musamman, inda ya nuna kin amincewarsa da tayin da jam’iyyar PDP ta yiwa sanata Shekarau.