Sanata Ibrahim Shekarau dake wakiltar Kano ta tsakiya, ya koka kan makudan kudin da ake kashewa da sunan tafiyar da al’amuran gwamnati, inda ya shawarci shugaba Bola Tinubu kan bukatar rage yawan ‘yan majalisar dokokin taraiyya da ake dasu.
Majalisar ta kunshi Sanatoci 109 da kuma ‘yan Majalisar Wakilai 360.
Sai dai a hirar da aka yi da sanata Shekarau a gidan Talabijin na Channel TV ya ce a halin da ake ciki, kasar nan bata bukatar zaurikan majalisun dokoki guda biyu.
Ya ce duk da kasancewar tsarin dimukuraddiya ya bada damar a shigar da kowa cikin gwamnati, to sai dai tsarin da kasar nan ke akai, na ‘yan majalisa kimanin 500 na zukewa gwamnati makudan kudi.
Tsohon gwamnan na Kano ya kuma bada shawarar rage yawan hukumomin da ake dasu sakamakon yawan kudin da gwamnati ke kashewa wajen tafiyar dasu, a maimakon yiwa jama’a aiki.