Dan takarar shugaban kasa a karkashjin jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa jam’iyyar ta kasa cika wasu daga cikin bukatun da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya gabatar masa.
Kwankwaso Ya shaida wa BBC Hausa cewa babu wata baraka tsakaninsa da Shekarau, wanda shine dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam'iyyar.
Kwankwaso ya mayar da martani ne kan labarin dake cewa Shekarau na iya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP saboda rashin cika sharuddan yarjejeniyar da suka cimmawa tsakaninsu kafin komawar Shekarau zuwa jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso ya ce babu wata yarjejeniya da ba a cika ba tsakaninsa da shekarau, sai dai abunda ya shafi ta ‘yan takara domin galibin mutanen da Shekarau ya kawo domin dorasu akan takarar abun ba zai yuwu ba a lokacin sakamakon kurewar lokaci, la’akari da ka’idar da hukumar zabe ta shimfida.
A wani bangaren kuma,Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya amince da nadin Dr. Abdulmumin Jibrin Kofa da Barista Ladipo Johnson a matsayin masu magana da yawun yakin neman zaben sa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Kwankwaso, Ibrahim Adamu ya fitar a ranar Laraba, ta ce Dr Abdulmumin Jibrin Kofa, wanda ya kasance tsohon dan majalisar wakilai ne a kananan hukumomin Kiru da Bebeji, yana da gogewa a fannin gudanar da yakin neman zabe da kuma hulda da jama’a.
A cewar sanarwar, shima Barister Ladipo Johnson fitaccen mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ne kuma tsohon dan takarar gwamna da na majalisar wakilai a jihar Legas.
Ya kammala karatunsa na digiri a Jami'ar Jihar Legas sannan kuma shine shugaban wata kungiya mai rajin samar da cigaba ta Johnson.