On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Sanata Ike Na Fuskantar Dauri Rai Da Rai

SENATOR IKE EKWEREMADU

Ana zargin tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu tare da Mai Dakinsa Beatrice da aikata lefin Hada Baki domin cire wasu sassa na jikin wani yaro a kasar Burtaniya, wanda zai sa ya iya fuskantar Daurin Rai da rai a kasar, Muddin aka same shi da aikata lefin, kamar yadda kunshe cikin sabbin dokokin yaki da aikata lefukan Bautarwa na shekarar 2015.

An cafke Ma’aurantan ne biyo bayan wani bincike da Tawagar Kwararrun Yansanda masu gudanar da bincike na birnin Landan suka gudanar, inda kuma aka gurfanar dasu a gaban kotun Majistare ta Uxbridge a jiya, Sai dai kuma  Kotun taki bayar dasu beli, inda ta dage zamanta zuwa ranar 7 ga watan Gobe.

Am wani bangaren kuma ana cigaba da samun zagayawar wata wasika a kafafen sadarwa na zamani, Wadda ke nuni da cewar tun a  cikin watan Disambar Bara ne, Sanata Ike ya aikewa  Ofishin Jakadancin Burtaniya wasikar neman Takardar Biza domin yin bincike akan dashen ‘Kodar da za’a yiwa  wata  Yarsa.

Masu gabatar da kara na Kotun sun baiyana cewa Sanata Ekweremadu da Maidakinsa  ana tuhumarsu  da lefin daukar  yaro dan shekara 15 daga nan Najeriya zuwa kasar Burtaniya da ikirarin cewa yaje  kasar nan  domin ceton rai, to sai dai kuma bincike na zahiri ya gano cewa an kaishi kasar nan domin cire wasu sassa  na jikinsa.

Masu gabatar da kara sun baiyanawa kotun cewa  Ekweramadu  Ya nemarwa yaron Fasfo a bisa cewar dan shekaru 21 a duniya amma bincike ya tabbatar da cewa shekararsa 15.