Rahotanni na baiyana cewa, An halaka jami’an yansanda da kuma Dogarawan Sanata Ifeanyi Uba da har yanzu ba’a tantance yawansu ba, akan hanyar Enugu Ukwu dake cikin karamar hukumar Njikoka a jihar hukumar Anambra.
Wata majiya ta fadawa manema Labarai cewa, Yan ina da kisan sun bude wuta akan ayarin motocin sanatan, inda suka kashe jami’an yansanda da kuma dogarawan sanatan masu yawan gaske.
Duk da cewar kawo yanzu babu cikakken labarin yadda abun ya faru a daren jiya, sai wata majiya na baiyana cewa Makasan sunyi yunkurin halaka Sanatan ne.
Kakakin rundunar yansandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai tabbatar da adadin wadanda abun ya ritsa dasu ba kawo yanzu da muke baku labarin.