Sanatan Adamawa ta Arewa da kotu ta sauke shi daga kan kujerarsa, Elisha Abbo, Ya zargi shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio da zama kanwa uwar gami a hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, na sauke shi daga kan kujerarsa.
A jiya ne kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta soke zaben da aka yiwa Sanata Elisha Abbo na jam’iyyar APC, ta re da aiyana dan takarar jam’iyyar PDP Amos Yohanna a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben kujerar sanatan.
A martanin da ya mayar kan hukuncin da kotun ta yanke, Sanata Elisha Abbo ya zargi shugaban majalisar dattawa Sanata Akpabio da yin uwa da makarbiya wajen ganin kotun ta yanke hukuncin, Ya kuma ce akwai ragowar wasu sanatoci guda hudu da basu zabi Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ba, da suma kotun zata sauke su daga kan kujerunsu.
Ya kara da cewar sanata Orji Uzor Kalu na jam’iyyar APC mai wakiltar Abia ta arewa, shin kan sahun gaba da kotu zata sauke daga kan kujerarsa.
Sai dai ya bukaci magoya bayansa dasu kwantar da hankalinsu, tare da cin alwashin sake neman kujerar sanatan a shekarar 2027.
Sai dai a martanin da shugaban majalisar dattawan ya mayar, ya musanta cewar yana da hannu a hukuncin da aka yanke, inda ya baiyana cewar babu wani dalili da zai sa shi ya rika yiwa abokan aikinsa wani bita da kulli.