Sanata Dino Melaye wanda ya kasance Mai magana da yawun Dan Takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, Yace rashin katabus din da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke dashi, Ya cutar da damar da Asiwaju Bola Tinubu keda ita na bashi damar zama shugaban kasa.
Dino wanda ya baiyana haka yayin hirarsa da gidan Talabijin na Channels ta cikin shirinsu na Siyasa a yau, Yace gazawar jam’iyyar APC mai mulkin kasa wajen warware matsalolin tattalin arzikin kasa dake addabar Najeriya, Hakan tasa daukacin ‘yan takarar da jam’iyyar ke dasu ba zasu yi kasuwa a tsakanin ‘yan Najeriya ba.
A wani bangaren kuma, Shugaban Gamaiyyar kungiyoyin yada manufofin Asiwaju da kuma Shettima ta kasa, Adebayo Shittu, Ya baiyana kalaman Sanata Dino Melaye, a matsayin wani abu na nishadi , inda yace Tinubu ne dan takarar shugaban kasa bawai Shugaban kasa Buhari ba.