Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya tabbatar wa ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa jihohin Tiga da Gari daga nan Jihar Kano cewa Majalisar za ta yi wa kowanne bangaren adalci a lokacin sake duba kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.
Sanata Barau ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan kungiyar karkashin jagorancin Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake zauren majalisar a ranar Laraba.
Wata sanarwa da kakakin sa , Ismail Mudashir ya fitar, ta ce Barau, wanda ke shugabantar kwamitin majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulkin kasar, ya bayyana cewa zauren majalisar na 10 zai bai wa dukkanin kungiyoyin da ke ba da shawarar samar da karin jihohi dama domin su baiyana ra’ayinsu.
Shima a nasa jawabin, Sanata Mas’ud El jibrin Doguwa ya jaddada bukatar dake akwai na samar da jihohi biyu daga jihar Kano. Ya ce a cikin shekaru 40 da suka gabata, suna bayar da shawarwarin raba jihar Kano bisa la’akari da girmanta da yawan al’ummarta domin a samar da cigaban da ake muradi.