Kungiyar masu kamfanonin kwasar shara a Najeriya (AWAMN) ta yi kira ga gwamnatocin Jihohi da na tarayya da su samar da asusu na musamman domin sarrafa shara.
Shugaban AWAMN, Mista Olugbenga Adebola, ne ya yi wannan roko a lokacin kaddamar da shugabancin kungiyar, a Ikeja dake jihar Legas.
Adebola ya bayyana sarrafa sharar gida a matsayin wani muhimmin bangare na tattalin arziki da ke bukatar kudade na musamman don tabbatar da dorewar muhalli.
Ya ce masu tafiyar da harkokin sharar za su hada kai da gwamnati a dukkan matakai domin kawo sauyi a harkar sarrafa shara a kasarnan.
A cewarsa, Ζ™ananan lamuni zai basu damar saka hannun jari don samar da yanayi mai dorewa.
Shugaban ya bayyana ingantacciyar sarrafa shara a matsayin ayyukan tallafawa kiwon lafiya domin zama rigakafi, wanda zai rage zazzabin Lassa da cizon sauro da tabbatar da ingantaccen muhalli.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki nauyin mambobinta zuwa tarurrukan gida da waje da horo da yawon bude ido, domin hakan zai kara musu karfin gwiwa da kwarewa.
A cewarsa, hakan zai taimaka masu sarrafa sharar gida wajen cin gajiyar sabbin cigaban fasaha wadanda za su inganta aikinsu, da rage yawan matsaloli da kuma inganta kudaden shiga.