Hukumar bada agajin gaggawa ta ksa NEMA tace kawo yanzu ambaliyar tayi ajalin mutane samar da 300 a sassa daban-daban na kasarnan a bana.
Shugaban hukumar ta NEMA, Mustapha Ahmed,shine ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani da masu ruwa da tsaki a Abuja.
Yace ana samun rotanninn ambaliyar ruwa sama da guda 50 a kowacce rana inda al’marin ya shafi sama da garuruwa 100.
Yace adadin iftila’in na cigaba da karuwa a kullum yana mai gargadin cewa ambaliyar ruwa a shekarar 2022 zatayi muni fiye da wadda aka fuskanta a shekarar 2012 lokacin da ak samu mutuwar mutane 363 sannan mutane milliyan 2 da dubu dari 2 suka rabu da matsugunansu sanadiyar ambaliyar ruwa a shekarar.