Sama da Gidaje Dubu biyu da Dari Biyar ne suka salwanta a gabashin Kasar Sudan, sakamakon wata ambaliyar ruwa da aka samu, wadda tayi sanadin raba dubban mutane da muhallansu, kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka baiyana.
Kazalika karin wasu gidaje 546 sun rushe sakamakon Mamakon ruwan sama da ake samu kamar da bakin kwarya a yankunan dake kusa da Kogin Nilu a ranar Alhamis.
Tun bayan faduwar daminar bana a cikin watan Mayu, Ofishin kula da aiyukan jin kai na majalisar dinkin duniya yayi kiyasin cewa mutane sama da Dubu 38 ne amabaliyar ruwa zata shafa a gabashin Afrika.
A mafi akasarin lokuta Damina na kaiwa har cikin watan Satumba a kasar Sudan, inda kuma aka fi samun ambaliyar ruwa a tsakanin watannin Augusta zuwa Satumba.
Koda a bara, mutane sama da Dubu 314 ne ambaliyar ruwa ta shafa a kasar ta Sudan kamar yadda Majalisar Dinkin duniya ta baiyana.