Mai shari’a Adebukola Banjoko na babbar kotun birnin tarayya
Kwanaki biyar bayan majalisar magabatan kasarnan ta yi wa wasu mutane 159 afuwa, tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye da Tsohon Gwamna Jolly Nyame na Jihar Taraba da wasu mutane 157 har yanzu ba su shaki iskar ‘yanci ba.
Rahotonni sun nuna cewa ba za a sake su daga cibiyoyin gyaran hali da ake tsare da su ba har sai Ministan Shari’a kuma Atoni-Janar na Tarayya Abubakar Malami ya ba da izini.
Mai shari’a Adebukola Banjoko na babbar kotun birnin tarayya ya samu Dariye da Nyame da laifin badakalar kudi a shekarar 2018 da suka kai Naira billiyan 1.162 da billiyan 1.6.
Sai dai da yake magana kan ci gaba da tsare wadanda aka yankewa hukuncin, kakakin hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa reshen babban birnin tarayya, Humphrey Chukwuedo, ya ce an jinkirta sakin su ne saboda ba'a samu amincewar Ministan Shari'a ba.