Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace nan bada jimawa hada-hadar kasuwanci zata kankama a sabuwar Kasuwar magunguna ta zamani ta Kanawa dake dangwauro da zarar an budeta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin day a jagoranci raba takardun shaidar mallakar shagunan Kasuwar a hukumance. Ya umarci wadanda suka mallaki rukunin farko na shugunan sama da guda 700 akan su gaggauta fara sanya sauran kayykin da suke bukata.
Yace nan da wani lokaci kalilan za’a bude kashin farko na sabuwar Kasuwar ta magunguna ta zamani dake da wurin ajiya na karkashin kasa da tsaro da sauran kayyakin bukatu da hukumomin tsaro.
Yace kasuwar zata taimaka wajen habaka tattalin arziki baya ga taimakawa wajen yaki da miyagun kwayoyi da jabun magunguna a kasarnan.
Samar da kasuwar dai wani shiri ne na gwamnatin tarayya hadin gwiwa da gwanatocin jahohi da bangarorin zuba jari na kafa kasuwannin hada-hadar magunguna a killace a Kano da Lega da Abad a Onicha.
Da yake zanatawa da manema labarai yayin taron daya daga cikin Iyayen hadakar kungiyoyin masu hada-hadar magunguna a Jihar Kano, Alhaji Dahiru Abdullahi Matazu Matazu, ya bukaci sauran masu harkokin magunguna su kara kallon kudirin komawa sabuwar kasuwar da kyakykyawar niyya domin amfani kansu da cigaban kasa da zamantakewar al’umma idan akayi la’akari da matsalolin da ake fuskanta a baya.
''Fatana su 'yan uwa da suke cikin wannan sana'a mu gane cewa wannan kudiri na dawowa nan, wani kudiri ne da duk wani dan magani da ya shekara arba'in zuwa yanzu ko fiye da haka yasan ana samun sabani tsakaninmu da hukumomi akan maganar wurin da ake sana'a sai muka samu cikin ikon Allah gwamnatin tarayya ta yarda a gina kasuwar magani a legas da Aba da Anicha, kuma nan Kano shi mai girma gwamna yasan tataburzar da muke ciki saboda haka a kasarnan shi ya fara bada fili domin cika wannan kudiri'' acewar Matazu.
''Ganduje zamu fara dagawa tuta saboda wannan kokari muna fatan Allah yasa wannan Kasuwa ta ba wa kasarmu zamanj lafiya a samu magani mai inganci.