Shugabannin kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC sun bayar da umarnin dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da samar da wutar lantarki cikin gaggawa a jihar Imo yayin da aka fara yajin aikin a jihar daga ranar Laraba 8 ga watan Nuwamba 2023
Shugabannin kungiyoyin biyu sun cimma wannan matsaya ne bayan wani taron majalisar zartarwa ta kasa na musamman da aka gudanar ranar Talata a Abuja.
A cikin sanarwar bayan taron da shugaban TUC, Festus Osifo ya sanya wa hannu da Mataimakin Shugaban NLC, Adewale Adeyanju, kungiyoyin sun kuma ayyana yajin aikin gama-gari a fadin kasarnan daga ranar Talata mai zuwa, 14 ga Nuwamba na 2023.
Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan cin zarafin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a makon jiya a jihar Imo.