Wakili a Hukumar Kwallon kafa ta duniya kuma dan kwamitin gudanarwa na Hukumar Kwallon kafa ta nahiyar Afrika, Amaju Pinnick ya mika ragamar tafiyar da Hukumar Kwallon kafa ta kasa NFF ga sabon shugaban hukumar Ibrahim Musa Gusau.
Gusau ya samu nasara a zaben shugabannin Hukumar da aka gudanar a ranar 30 ga watan da ya gabata a birnin Benin na kasar Edo.
Shugaban hukumar mai barin gadoyayi kira ga jami’an gudanarwa na hukumar da sauran ma’aikata dasu baiwa sabon shugaban hukumar cikakken goyon baya kamar yadda suka bashi a lokacin da yake shugabantar hukumar.
Kazalika yace kofarsa zata cigaba da kasancewa a bude domin neman shawara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso