On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Sabon Kamfanin Jirgin Najeriya Zai Kawo Sauyi Da Cigaba - Fadar Shugaban Kasa

Muddin ba wani sauya aka samu na gaggawa ba, Ministan sufurin jiragen sama ya ce jirgin saman Najeriya Air zai iso kasarnan a gobe Juma'a.

Matakin dai nada nufin kaddamar da kamfanin sufurin jiragen sama na kasa, Nigerian Air kafin wa'adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare a ranar 29 ga watan Mayu.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channel a yayin da ake ta shakku kan yiwuwar fara aikin kamfanin a gwamnatin Buhari, Sirika ya tabbatar da cewa zai  fara aikin kafin ranar Litinin.

Bayanai a daren jiya na cewa jirgin da aka riga aka yi wa fenti kalar Najeriya zai iya isowa daga kamfanin Ethiopian Airlines domin yin gwaji.

A wanibangaren kuwa, har yanzu babu tabbaci ko anyi watsi da umarnin da aka bayar kan dakatar da hannun jarin  kamfanin duk da cewa har yanzu ba a ji wani gagarumin kuduri na kalubalantar tsarin rabon hannayen jarin ba.

Shi kuwa babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai ga shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ta cikin shirin Sunrise Daily na gidan  Talabijin na Channels, ya ce sabon kamfanin Nigeria Air zai kawo babban sauyi da kuma alfanu ga 'yan Najeriya da kowa zai yaba da hakan.

Yayin da yake yabawa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika bisa jajircewarsa wajen ganin kamfanin ya fara aiki, ya ce ‘yan Najeriya da dama ne za su ci gajiyar aikin.

Garba ya amince da  cewa kalubale da dama sun kawo cikas ga aikin. Sai dai a cewarsa hadin gwiwar da akayi da kamfanin jiragen saman Ethiopian Airways na da matukar amfani ga kasarnan.