
A ranar Laraba ne rundunar Yansanda Ta fitar da sanarwar kama jami'an yansanda domin yin bincike a kansu.
Rundunar ‘yansanda ta kasa ta kori jami’an ‘yansandan nan dake tsaron lafiyar fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara saboda samunsu da lefin barnatar da harsashin bindiga a wofi.
Kakakin rundunar yansanda ta kasa,Olumiyiwa Adejobi ne ya baiyana matakin da rundunar ta dauka a shalkwatarta dake Abuja ranar Alhamis, biyo bayan kammala binciken da aka yi kan jami’an yansandan da abun ya shafa.
Dogarawan Mawakin da abun ya shafa sun hada da Sergent Abdullahi Badamasi sai Sergernt Isah Danladi , wanda aka gansu a cikin wani faifan bidiyo da aka dauka a ranar 7 ga watan da muke ciki, Suna yin harbi cikin iska a lokacin da suke tare da mawakin siyasar.
Adejobi ya ce an sallami jami’an yansandan ne saboda nuna rashin da’a da kuma yin amfani da bindiga a wurin da bai kamata ba, da kuma bata harsashin bindiga